Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NARD) ta koka kan ƙarancin likitoci a ƙasar, inda ta bayyana cewa lissafi da aka gudanar ya nuna cewa duk likita ɗaya yana kula da mutane 9,083 – lamarin da ta ce ya saɓa da ƙa’idar duniya.
A wani jawabi da ta fitar a ranar bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai, ƙungiyar ta ce daga yau, 1 ga Oktoba 2025, ba za a ƙara bari likitocin kwararru su yi aiki fiye da awa 24 a jere ba.
NARD ta ce Najeriya na da yawan jama’a sama da miliyan 240, amma dukkan likitocin ba su wuce 11,000 ba, yayin da sama da likitoci 16,000 suka bar ƙasar cikin shekaru bakwai da suka gabata. Wannan, in ji ta, ya jefa sauran cikin gagarumin nauyi, inda suke yin aiki har sama da sa’o’i 100 a mako, abin da ke haifar da gajiya, kura-kurai a jinya da kuma barazana ga lafiyar su.
Ƙungiyar ta yi kira ga Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da ta aiwatar da tsarin maye gurbin kowane likita da ya tafi, da kuma samar da kariya kan yawan awanni a aiki. Ta bayyana cewa waɗanda suka zauna a ƙasar duk da ƙalubale “gaskiya jarumai ne” kuma suna bukatar a biya su daidai da gudummawar da suke bayarwa.
