Jam’iyyar APC ta yi watsi da kiraye-kirayen dawo da tallafin man fetur, tana mai gargadin ’yan Najeriya kan ’yan siyasar da ke alkawarin soke daya daga cikin manyan sauye-sauyen tattalin arziki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar.

Daraktan Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na APC na 2027, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce duk wani dan siyasa da ke neman kuri’a da alkawarin dawo da tallafin man fetur yana yaudarar ’yan Najeriya.

Yari ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan alkawarin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, na kafa tsarin tallafi na musamman idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027. Ya ce tsarin tallafin mai ya kasance mai tsadar gaske kuma babu cikakken bayani kan yadda ake gudanar da kudaden.

Tsohon gwamnan Zamfara ya ce babu tanadin kudin tallafin man fetur a kasafin kudin shekarar 2023 da Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da shi kafin Tinubu ya hau mulki. Ya kuma ce tsarin tallafin ya shafi makudan kudade ba tare da samun sahihin bayanai kan adadin man fetur da Najeriya ke amfani da shi a kullum ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version