Jami’an Hukumar EFCC sun nufi karɓe gidan tsohon Ministan Shari’a na Tarayya, Abubakar Malami, da ke Maitama a Abuja a ranar Talata. Rahotanni sun ce jami’an sun isa wurin cikin motocin bas kusan biyar, dauke da makamai, tare da kulle hanyar shiga gidan.
An ce jami’an, karkashin jagorancin Folarin Dare, sun killace yankin gidan da ke No. 2 Koranakh Close, tare da hana shiga ko fita daga wurin. Wannan mataki ya hana mutane samun damar shiga gidan yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin.
Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na da nasaba da binciken da ake yi kan wasu zarge-zargen rashin gaskiya a harkokin kuɗi. Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana cikakkun bayanai kan lamarin ba.


