Gwamnatin Zamfara ta amince da biyan albashin watan Maris da wuri ga dukkan ma’aikatan gwamnati da masu karɓar fansho a fadin jihar, domin ba su damar yin shirye-shiryen bukukuwan Eid al-Fitr cikin sauƙi.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar, Muhammad Dantawasa, ya sanya wa hannu, gwamnatin ta ce an kammala duk shirye-shirye domin tabbatar da an biya albashi da fansho cikin gaggawa ga dukkan waɗanda abin ya shafa.
Gwamnan jihar, Dauda Lawal, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kula da jin daɗin ma’aikata da masu ritaya, tare da kira gare su da su ci gaba da goyon bayan manufofin gwamnati da kuma yin addu’ar zaman lafiya da cigaban jihar.


