Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da sabuwar ƙara ta Naira biliyan 10 a kan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) bisa zargin hana shi ganin iyalansa yayin da yake tsare.

A ƙarar da lauyansa, Ubong Akpan, ya shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar 13 ga Agusta, El-Rufai ya ce ICPC ta hana matarsa, Aichatou Asabe, da ɗansa, Abba El-Rufai, ziyartarsa.

Ya ce hana shi ganin iyalansa ya hana su kai masa abinci, magunguna da sauran muhimman abubuwan da yake buƙata yayin da yake tsare, lamarin da ya ce ya take haƙƙoƙinsa na ɗan’adam da kundin tsarin mulki ya tanada.

El-Rufai ya nemi kotu ta tabbatar da haƙƙinsa na samun damar ganin iyalansa da lauyoyinsa, tare da neman diyyar Naira biliyan 10 kan abin da ya bayyana a matsayin tauye masa haƙƙi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version