Firaiministan Faransa, Sébastien Lecornu, ya ajiye muƙaminsa ƙasa da kwana ɗaya bayan ƙaddamar da ƴan majalisar zartarwarsa, a wani lamari da ya girgiza siyasar ƙasar.
Lecornu ya bayyana murabus ɗinsa ne da safiyar Litinin 06 ga Oktoba, inda ya ce “ba a cika sharuɗɗan da suka dace ba da za su bani ikon ci gaba da zama firaiminista.” Ya kuma soki rashin haɗin kai da rashin yarda tsakanin jam’iyyun siyasa wajen cimma matsaya ta haɗin gwiwa.
Fadar Élysée ce ta tabbatar da murabus ɗin, bayan ganawar awa guda da Lecornu ya yi da Shugaba Emmanuel Macron a ranar Litinin.
Wannan mataki ya zo ne kwanaki 26 bayan naɗa Lecornu a matsayin firaiminista, sakamakon rugujewar gwamnatin da ta gabata ta François Bayrou.
Dukkan manyan jam’iyyun siyasa da ke majalisar dokokin ƙasar sun nuna rashin amincewarsu da sabuwar majalisar Lecornu, wadda suka ce ba ta kawo wani sabon salo ba daga gwamnatin da ta shuɗe. Sun kuma yi barazanar kada ƙuri’ar rashin amincewa, wanda hakan ya jefa Lecornu cikin matsin lamba mai tsanani tun kafin ya fara aiki sosai.
