Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da taron horaswa na kwana biyu ga masu wallafa labarai ta yanar gizo a Dutse, Jihar Jigawa, domin ƙarfafa ƙwarewa, ɗabi’a da ingancin aikin jarida a duniyar dijital mai saurin sauyi.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce kafafen yanar gizo ginshiƙi ne na dimokuraɗiyya, don haka ya zama wajibi su riƙa aiki bisa gaskiya, bin ƙa’idojin sana’a da dokokin ƙasa. Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na goyon bayan ci gaban aikin jarida da kare ‘yancin manema labarai.
Shugabannin NUJ da Ƙungiyar Kafafen Yanar Gizo sun yaba da taron, suna masu cewa horon ya zo a kan lokaci, kuma zai taimaka wajen samar da ‘yan jarida masu sanin doka, ɗabi’a da amfani da sabbin fasahohi yadda ya dace.
