Hukumar Kula da Hanyoyi ta Ƙasa (FRSC) ta bayyana cewa ta inganta cibiyar buga takardunta domin samar da matsakaicin lasisin tuƙi guda 15,000 a kowace rana, wanda hakan zai bai wa masu neman lasisi damar karɓar takardunsu nan take ba tare da jinkiri ba. Wannan mataki, a cewar hukumar, na daga cikin ƙoƙarinta na kawar da matsalar jinkirin da ake samu wajen karɓar lasisin tuƙi a faɗin ƙasar.

Kwamandan FRSC na ƙasa, Shehu Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara cibiyar buga takardun hukumar a birnin Abuja. Ya ce sabon tsarin zai taimaka wajen tabbatar da cewa duk masu neman lasisin tuƙi sun karɓa kafin tsakiyar watan Nuwamba, tare da rage cunkoso da tsaiko a tsarin bayar da lasisi.

Mohammed ya bayyana cewa FRSC za ta fara amfani da tsarin ɗaukar bayanan yatsu daga nesa, wanda zai bai wa hukumar damar buga lasisin tuƙi kai tsaye ba tare da buƙatar lasisin wucin gadi ba. Ya ce wannan sabuwar fasaha za ta inganta aikin hukumar da kuma tabbatar da cewa duk wani direba ya samu lasisinsa cikin sauri da sauƙi.

A cewarsa, wannan ci gaba babban nasara ne ga hukumar da kuma ’yan Najeriya baki ɗaya, domin zai kawo ƙarshen jinkiri da sauran matsalolin da suka dade suna addabar tsarin bayar da lasisin tuƙi a ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version