Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ayyana Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar. Yilwatda ya kuma ce zai goyi bayan Fubara domin wa’adi na biyu idan ya samu nasara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Yilwatda ya bayyana hakan ne a wani shiri na Channels Television, inda ya ce duk da cewa Fubara shi ne shugaban APC a Rivers, dole ne ya yi aiki tare da sauran jiga-jigan jam’iyyar a jihar. Wannan sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun saɓani na siyasa tsakanin Fubara da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kan jagorancin APC a Rivers.
Tun a watan Disamba ne Fubara ya sanar da komawa APC tare da bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar, matakin da Wike ya ƙi amincewa da shi. Yilwatda ya ce ba shi ke zaɓen wanda zai yi nasara a zaɓen fidda gwani ba, amma zai mara wa duk wanda ya lashe zaɓen jam’iyyar baya.
