Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya dawo Najeriya bayan shafe makonni yana hutu a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa. Ganduje ya iso filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagos a ranar Asabar da yamma.
Bayan isowarsa, ya wuce Abuja da misalin karfe 8 na dare a wannan rana. Wata sanarwa da shugaban ma’aikatansa, Muhammad Garba, ya fitar ta ce Ganduje na shirin fara jerin tuntuba da ganawa da masu ruwa da tsaki kan abubuwan siyasa da ke faruwa a jihar Kano.
Sanarwar ta kara da cewa Ganduje zai kuma shiga aikin rajistar mambobin APC ta yanar gizo da ake ci gaba da yi a fadin kasar. An bayyana cewa shirin, wanda ya kaddamar da shi tun yana shugaban jam’iyyar, na da nufin inganta bayanan mambobi da karfafa tsarin jam’iyyar APC, musamman a jihar Kano.
