Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Bankin Bayar da Lamunin Gidaje na Ƙasa (FMBN), Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi murabus daga mukaminsa. Rahotanni sun tabbatar da cewa ya kammala shirinsa na sauya sheƙa tare da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, inda ake sa ran zai koma jam’iyyar ADC a ranar Talata.
A cikin wasiƙar murabus ɗinsa mai ɗauke da kwanan wata 27 ga Maris, 2026, Gawuna ya bayyana cewa murabus ɗin nasa zai fara aiki nan take. Ya ce matakin ya yi dai-dai da umarnin Shugaban Ƙasa domin tabbatar da bin dokokin zaɓe gabanin harkokin siyasa masu zuwa.
Gawuna ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa damar da aka ba shi na yin aiki, yana mai cewa hakan wata dama ce ta ba da gudunmawa ga ci gaban bankin da ƙasa baki ɗaya. Ya kuma ce ya miƙa al’amuransa gaba ɗaya ga Allah tare da alƙawarin tabbatar da mika mulki cikin tsari kamar yadda doka ta tanada.
