Gwamnatin Jihar Filato ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 48 a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, bayan wani mummunan hari da ya auku a yankin Angwan Rukuba. Sanarwar da kwamishinar yaɗa labarai, Joyce Ramnap ta fitar, ta ce dokar za ta fara aiki daga tsakar dare na 29 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu, 2026.
Gwamnatin ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan wani hari da ya yi sanadin asarar rayuka tare da jikkatar mutane da dama a yankin Gari Ya Waye. Gwamna Caleb Mutfwang ya la’anci harin, yana mai kiran sa na rashin imani, tare da tabbatar da cewa ana kokarin cafke masu hannu a lamarin.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindiga sun kai harin ne kan babura suna harbe mutane kan hanya da masu sana’ar gefen titi, inda akalla mutum shida suka mutu yayin da wasu ke kwance a asibiti. Harin ya haddasa firgici a yankin, yayin da wasu matasa suka toshe hanya kafin jami’an tsaro su watse su.


