Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da rusa dukkan mambobin Majalisar Zartarwa ta jihar nan take. Matakin ya zo ne domin samar da dama ga duk wanda ke da sha’awar tsayawa takarar muƙaman zaɓe a zaɓuɓɓukan da ke tafe.
Gwamnan ya umurci dukkan kwamishinoni da su miƙa ragamar ma’aikatunsu ga Sakatarorin Dindindin kafin ranar Jumma’a, 3 ga Afrilu, 2026. Ya ce hakan zai tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati ba tare da tangarda ba.
A sanarwar da ofishinsa ya fitar, Zulum ya gode wa kwamishinonin bisa gudummawarsu da jajircewa wajen hidima ga al’ummar jihar. Ya ce matakin zai bai wa masu burin takara damar mayar da hankali kan shirinsu cikin sauƙi.


