Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da zaɓen mataimakinsa, Murtala Sule Galadima Garo, a matsayin abokin takararsa domin zaɓen gwamna na shekarar 2027. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin.

Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taro da masu riƙe da muƙaman gwamnatin tarayya daga Kano, wanda aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano da ke Abuja. Ya ce ya yanke wannan hukunci ne sakamakon aminci, jajircewa da kuma gudunmawar da Garo ke bayarwa wajen ci gaban jihar tun bayan hawansu mulki.

Gwamnan ya ce yana da cikakken yaƙini da ƙwarewa da jajircewar mataimakinsa, yana mai bayyana shi a matsayin amintaccen abokin aiki. Haka kuma ya buƙaci shugabannin jam’iyya, masu riƙe da muƙaman siyasa da magoya baya su ci gaba da haɗin kai yayin da gwamnati ke ƙarfafa nasarorin da ta samu tare da shirin babban zaɓen shekarar 2027.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version