Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, inda ya bayyana cewa an rantsar da sabon shugaban karamar hukumar Kumbotso, Ali Musa Hardworker.

Sanarwar ta ce gwamnan ya bukaci sabon shugaban da ya gudanar da ayyukansa cikin gaskiya da jajircewa, tare da mai da hankali wajen kawo ci gaba a matakin kasa. Ya kuma jaddada cewa ingantaccen shugabanci a kananan hukumomi na da muhimmanci wajen samun nasarar gwamnati.

A nasa bangaren, Ali Musa Hardworker ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin inganta rayuwar al’umma. Wakilinmu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa rantsarwar ta biyo bayan hukuncin babbar kotun Kano da ta soke zaben tsohon shugaban karamar hukumar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version