Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Hamisu Abdullahi, mai shekaru 38, bisa zargin yin ihu da kalmar “ba ruwa, ba wuta” yayin ziyarar gwamna Mohammed Umaru Bago a garin Suleja bayan sallar Idi.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce an kama mutumin ne bisa zargin yunƙurin kawo cikas ga ayyukan gwamnati, inda aka kai shi sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Minna a ranar 20 ga Maris, 2026.

Sai dai daga bisani an bayar da belinsa yayin da ake ci gaba da bincike. Rahotanni sun ce an tsare shi na tsawon kwanaki biyar kafin a sake shi, yayin da kuma wasu ke zargin an kama shi ne bisa umarnin gwamnan, lamarin da ba a tabbatar ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version