Farashin ɗanyen mai ya ragu a safiyar Laraba yayin da kasuwannin hannayen jari na nahiyar Asiya suka fara farfaɗowa. Hakan ya biyo bayan sanarwar da Iran ta bai wa Majalisar Ɗinkin Duniya cewa za ta bar jiragen ruwa na kasuwanci su rika wucewa ta mashigin Hormuz.
Iran ta bayyana cewa za a ba jiragen ruwa, ciki har da na ɗaukar mai, damar wucewa muddin sun nemi sahalewar hukumominta. Wannan mataki ya kawo sauƙi ga kasuwannin duniya da ke fargabar katsewar zirga-zirgar man fetur a yankin.
A gefe guda, shugaba Trump ya yi ikirarin cewa Iran ta amince ba za ta ƙera makamin nukiliya ba, sai dai hukumomin Tehran sun musanta hakan, suna cewa kalamansa na da nufin jan hankalin masu zuba jari da kuma tasiri kan farashin mai a duniya.


