Gwamnatin Jihar Cross River ta rufe makarantu 36 da ke aiki ba tare da izini ba a faɗin jihohin Calabar, Ikom da Ogoja. Makarantun sun haɗa da na firamare da sakandare, waɗanda aka gano suna gudanar da ayyuka ba tare da rajista ko amincewar ma’aikatar ilimi ba.

Kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Stephen Odey, ya tabbatar da matakin a Calabar ranar Talata 21 ga Oktoba, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici. Ya ce wasu mutane na ci gaba da yaudarar iyaye ta hanyar buɗe makarantu ba tare da izinin hukuma ba, abin da ke barazana ga ingancin ilimi a jihar.

Odey ya bayyana cewa kwamiti na musamman da aka kafa domin yaki da irin waɗannan makarantu ne ya aiwatar da rufewar, tare da gargadin cewa gwamnati ba za ta sake lamunce wa irin waɗannan “makarantu masu ɓoyayyen aiki” ba. Ya ce an fara bincike a yankunan ilimi uku na Calabar, Ikom da Ogoja, kuma za a ci gaba da aikin a sauran ƙananan hukumomi.

Kwamishinan ya kuma shawarci iyaye su rika tabbatar da matsayin izinin kowace makaranta kafin su saka ‘ya’yansu. Ya ce gwamnatin jihar ta kuduri aniyar tabbatar da cewa duk makarantu da ke aiki a Cross River sun samu cikakkiyar rajista da amincewar gwamnati domin kare martabar ilimi a jihar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version