Gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya sanya almajirai 4,500 cikin makarantun tsangaya na zamani, domin rage yawan yaran da ke yawo a tituna da kuma ba su damar samun ilimin addini, na zamani da sana’o’in dogaro da kai.

Babban Sakataren Hukumar Ilimin Tsangaya ta jihar, Dakta Abubakar Maje Hamisu, ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kan Alarammomi kan sabon tsarin. Ya ce gwamnati ta gina manyan makarantun tsangaya guda uku a Dutse, Kafin Hausa da Ringim.

Dakta Maje ya ce gwamnati za ta rika bai wa Alarammomi alawus a duk wata, tare da tallafa musu da kayan aikin noma da injinan samar da ruwa masu amfani da hasken rana. Ya kuma ce za a kafa dokar hana almajirai yawo da bara a babban birnin jihar, sai waɗanda ke karatu a makarantun da gwamnati ta amince da su.

Ya ce Jigawa na da makarantun Tsangaya na gargajiya 5,481, da 130 na haɗaka, bakwai na zamani da kuma manyan makarantun Tsangaya uku. Gwamnatin ta kuma ware Naira miliyan 480 domin gyara da faɗaɗa wasu makarantu shida, inda za a ƙara ɗalibai 1,500 ƙarƙashin shirin almajiranci.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version