Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce karin kudaden da jihar ke samu daga Asusun Tarayya a karkashin Shugaba Bola Tinubu ya ba ta damar biyan Naira biliyan 18 daga cikin bashin fansho da alawus da ta gada.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Ahmed Maiyaki, ya ce gwamnatin Gwamna Uba Sani ta gaji bashin fansho da alawus na kusan Naira biliyan 24, baya ga basussukan cikin gida da na kasashen waje.
Ya ce karin kudaden ya kuma taimaka wajen bunkasa ayyukan more rayuwa, inda a halin yanzu ake gudanar da ayyukan gina hanyoyi 115 a kananan hukumomi 23 na jihar. Fiye da rabin ayyukan sun kammala, wadanda suka shafi sama da kilomita 1,400 na hanyoyi.
Maiyaki ya kuma ce kasafin kudin noma ya karu daga Naira biliyan 1.4 a shekarar 2023 zuwa sama da Naira biliyan 100 a 2026. Ya ce gwamnatin jihar ta kara zuba jari a ilimi, lafiya, sufuri da tsaro, yayin da ta ce babu rikicin addini da aka samu a jihar cikin shekaru uku na mulkin Gwamna Uba Sani.
