Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe fiye da Naira biliyan 4.9 domin aiwatar da muhimman ayyuka da za su farfado da harkar ilimi a fadin jihar. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar bayan taron majalisar zartarwa karo na 33 da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta.

A cewar sanarwar, ayyukan da aka amince da su sun hada da gyaran Makarantar Fasaha ta Gwamnati da ke Ungogo (mataki na biyu), biyan bashin masu samar da abinci ga makarantun kwana, da kuma samar da kayan koyarwa ta hanyar buga su a kamfanin buga takardu na jihar.

Haka kuma, gwamnati ta amince da kammala da kuma sanya kayan aiki a ɗakin karatu na zamani (e-library) na Kwalejin Ilimi da Shirye-shiryen Farko ta Jihar Kano, tare da gudanar da ayyukan tantancewa a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano (Kano Polytechnic).

Gwamnatin ta kuma amince da sayen kayan ofis da kujeru ga Jami’ar (Northwest University) domin inganta ayyukan karatu da gudanarwa. Gwamna Abba ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da saka hannun jari a ilimi, yana mai cewa “ilimi shi ne ginshikin ci gaban al’umma.”

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version