Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da rasuwar fitaccen mawakin siyasa, Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waka, yana da shekaru 47 a duniya. wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Lahadi.
Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi. Iyalan marigayin sun ce za a binne shi a kauyen Tsanni da ke karamar hukumar Batagarawa ta Jihar Katsina da karfe 5 na yamma.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, musamman mahaifiyarsa, da abokansa, makusantansa, masoyansa da daukacin al’ummar Jihar Kano. Ya bayyana Kosan Waka a matsayin dan asalin Katsina mazaunin Kano, wanda wakokinsa suka wuce siyasa, inda suka taimaka wajen karfafa hadin kai, al’adu da wayar da kan jama’a.
Gwamnan ya roki Allah SWT Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata kabarinsa, Ya shigar da shi Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansa karfin jure wannan babban rashi. Gwamnatin ta ce gudunmawar Kosan Waka wajen bunkasa sadarwar siyasa da nishadantar da al’umma ba za a manta da ita ba.


