Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani gini da ake zargin za a mayar da shi gidan wasan kwaikwayo (Film House) a unguwar Dorayi Karama, cikin Karamar Unguwar Bello da ke Karamar Hukumar Gwale. Hakan ya biyo bayan zargin karya wasu ka’idojin gine-gine da gwamnati ta ce an yi a wurin.
Shugaban kwamitin kar-ta-kwana na kula da gine-ginen da ba su bi ka’ida ba, kuma Babban Daraktan Hukumar KANGIS, Dakta Dalhatu Aliyu Sani, ya ce an rufe ginin ne saboda rashin cika wasu sharuddan da suka dace, musamman kasancewar wurin yanki ne na zama ba na masana’antu ba. Ya kuma ce masu aikin ba su nemi sahalewar hukuma kafin fara ginin ba.
Dakta Dalhatu ya kara da cewa an tarar da dakunan kwana a cikin ginin inda maza da mata ke kwana, lamarin da ya sa aka dakatar da aikin tare da gargadin masu ginin kada su bude wurin har sai gwamnati ta kammala tattaunawa da nazari kan lamarin. Wakilin Kakaki24, Abba Isa Muhammad, ya rawaito cewa kwamitin ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da bibiyar gine-ginen da ake gudanarwa ba bisa ka’ida ba a fadin jihar.
