Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da kashe sama da Naira biliyan 4.05 domin gyaran asibitoci guda bakwai a fadin jihar. Mai ba da shawara kan harkokin shari’a kuma Kwamishinan Shari’a, Alhaji Junaidu Marshall, ne ya bayyana haka bayan taron majalisar zartarwa da Gwamna Nasir Idris ya jagoranta a Birnin Kebbi. Asibitocin da za su amfana sun haɗa da na Kambaza, Suru, Kamba, Dirin-Daji, Kangiwa, Koko da Yauri, yayin da wasu asibitoci 16 tuni aka kammala gyaransu. Gwamna Idris ya tabbatar da cewa kafin ya kammala wa’adinsa, za a gyara dukkan asibitoci 30 na jihar tare da samar musu da kayan aiki na zamani.

Bugu da ƙari, majalisar ta amince da biyan Naira miliyan 570 ga Hukumar Kula da Lafiya ta Kananan Hukumomi (KECHEMA) domin yin rijistar mutane 45,000 daga cikin masu rauni a cikin Kundin Talakawa na Jihar. Wannan zai bai wa kowace gunduma 225 damar shigar da aƙalla mutane 200 cikin tsarin kiwon lafiya mai sauƙin biya. Haka kuma, jihar ta samar da kuɗaɗen haɗin gwiwa da Bankin Duniya don gyaran cibiyoyin kiwon lafiya 73, tare da ƙarin gyaran wasu 42 a matakin ƙaramar hukuma.

Haka nan, gwamnatin ta amince da Naira miliyan 407.5 a matsayin kuɗin farawa ga Hukumar Magunguna da Kayan Kiwon Lafiya ta Jihar Kebbi, domin samar da magunguna masu sauƙin samu da rahusa. A gefe guda kuma, majalisar ta amince da kafa Hukumar Kididdiga ta Jihar Kebbi tare da Naira miliyan 900 a matsayin kuɗin farawa, inda ta naɗa Farfesa Umar Usman a matsayin Babban Jami’in Kididdiga na farko. Hukumar za ta tabbatar da samar da bayanai ingantattu domin tsara da sa ido kan shirye-shiryen ci gaban jihar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version