Gwamnatin Tarayya ta gabatar da sabon tayin ƙarin albashi har na kashi 40% ga malamai membobin ASUU, a wani yunƙuri na kauce wa yajin aikin da ke tunkaro jami’o’in ƙasar. Wannan na zuwa ne bayan zaman NEC na ASUU da aka gudanar a Abuja, inda shugabannin rassan ƙungiyar suka cimma matsayar komawa tattaunawa da gwamnatin Tarayya.

Wata majiya daga ASUU ta bayyana cewa shugabannin rassan za su koma wuraren aiki domin sanar da mambobinsu halin da ake ciki. Tuni wa’adin wata ɗaya da kungiyar ta ba gwamnati ya ƙare ranar Asabar, lamarin da ya ƙara tayar da hankula a tsakanin malamai da ɗaliban jami’o’in ƙasar.

A cewar majiyar, “Sun gabatar da tayin ƙarin albashi 40%. Za mu koma mu sanar da mambobi. Tattaunawa za ta ci gaba mako mai zuwa.” Ministan ilimi Tunji Alausa, wanda ke ƙasashen waje, ya jaddada cewa gwamnati ta bi yawancin bukatun ASUU, tare da umarnin Shugaba Tinubu cewa ba a so a sake samun yajin aiki. Kakaki24 ta tabbatar da cewa bangarorin biyu sun ɗauki matakin ci gaba da tattaunawa.

ASUU ta sha nuna rashin jin daɗi kan jinkirin aiwatar da yarjejeniyar 2009, biyan albashin da aka rage da kuma kuɗaɗen inganta jami’o’i. Haka kuma, Ƙungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana goyon bayanta ga ASUU tare da gargadin cewa za ta shiga cikin lamarin idan gwamnati ta gaza cika alkawurra.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version