Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin aiwatar da harajin kashi 15 cikin 100 kan shigo da man fetur da dizal daga ƙasashen waje. Hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa (NMDPRA) ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce aiwatar da wannan haraji “ba ya cikin tsare-tsare a halin yanzu.” A baya, rahotanni sun nuna cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da harajin mai suna ad-valorem a kan man fetur (PMS) da dizal (AGO), sai dai an janye matakin domin kauce wa tashin farashin mai da kuma yiwuwar karancin sa a kasuwa.

Hukumar NMDPRA ta tabbatar da cewa akwai wadataccen man fetur, dizal da iskar gas a ƙasar, waɗanda ke fitowa daga matatun cikin gida da kuma shigo da su daga waje. Ta ce wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da ci gaba da wadatar mai a tashoshin rarrabawa, musamman a lokutan da ake buƙatar sa sosai.

Hukumar ta kuma roƙi ’yan kasuwa da masu tashoshi da su guji boye mai ko ƙara farashi ba bisa ka’ida ba, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da sa ido kan harkokin rarraba mai don kauce wa kowace irin tangarda. Haka kuma ta tabbatar da aniyar ta wajen tabbatar da tsaron makamashi da wadatar mai a fadin ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version