Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta fara wani shiri a Jihar Jigawa domin mayar da aƙalla yara 5,000 da suka daina karatu ko kuma ba su taɓa shiga makaranta ba zuwa makarantu. Ta bayyana hakan ne yayin duba yadda ake gudanar da tantance ilimi ta ƙasa a Ringim.
Ta ce Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fara tantance matakin ilimin ɗalibai a makarantun firamare da sakandare domin auna yadda suke fahimtar abin da ake koya musu, tare da amfani da sakamakon wajen tsara manufofin inganta ilimi. Ta ƙara da cewa an gudanar da jarabawar cikin tsari ba tare da wata matsala ba.
Farfesa Suwaiba ta ce sakamakon tantancewar zai taimaka wajen inganta tsarin koyarwa da ilmantarwa a faɗin ƙasar. Ta kuma jaddada cewa gwamnatin tarayya na haɗa kai da hukumomi daban-daban domin dawo da yaran da ba sa zuwa makaranta cikin tsarin ilimi.
