Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya goyi bayan kira ga ƙasashen waje da su taimaka wajen dakile kashe-kashe a Najeriya, yana mai cewa gwamnatin tarayya ta kasa cika hakkin kare rayukan ‘yan ƙasa. Ya bayyana haka ne a wajen taron Plateau Unity Christmas and Praise Festival da aka yi a Dwei-Du, Jos, ranar Juma’a 28 ga Nuwamba 2025.
Bechi Hausa ta tattaro cewa Obasanjo ya ce fasaha da tauraron dan adam sun isa gano duk wanda ke aikata kashe-kashe a ƙasar, amma gwamnati bata yin abin da ya kamata. Ya ce ba za a yarda a rika kare laifuka da hujjar addini ko kabila ba domin “dukkan ‘yan Najeriya ake kashewa, kuma wannan abin kunya ne ga ƙasa.”
Tsohon shugaban ya ce idan gwamnati ta kasa kare jama’a, ‘yan ƙasa na da damar neman taimakon ƙungiyoyin duniya. Ya yi Allah-wadai da tattaunawa ko ba da kudade ga ‘yan ta’adda, yana mai cewa gwamnati dole ta tsaya tsayin daka don dakatar da kashe-kashe a ko ina a kasar.
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya yi kira da a tashi tsaye wajen neman zaman lafiya da haɗin kai, yana mai cewa rashin haɗin kai ne ya hana jihar cimma ci gaba yadda ya kamata. Ya nemi al’umma su bar abin da ke raba su, su rungumi abin da ke haɗa su domin zaman lafiya da kare rayuka.
