Wani bincike ya nuna cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu amincewar rancen dala biliyan 11.4 daga Bankin Duniya tsakanin Yunin 2023 zuwa Yunin 2026. Adadin ya kai kusan kashi 78 cikin 100 na dala biliyan 14.59 da aka amince wa gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a tsawon shekaru takwas.

Sai dai bayanan Bankin Duniyar sun nuna cewa daga cikin dala biliyan 11.4 da aka amince da su, an fitar da dala biliyan 2.32 kacal, yayin da sauran dala biliyan 8.41 ke jiran fitarwa. Yawancin kuɗaɗen an ware su ne domin sauye-sauyen tattalin arziki, noma, ilimi, lafiya, wutar lantarki, fasahar sadarwa da shirye-shiryen kare marasa galihu.

Masana tattalin arziki sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan karuwar bashin, inda wasu suka ce bashi ba matsala ba ne idan an yi amfani da shi yadda ya kamata, yayin da wasu suka yi gargaɗin cewa ci gaba da karɓar rance ba tare da ƙarfafa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ba na iya jefa ƙasar cikin matsin tattalin arziki. Bashin Bankin Duniya ya kai kusan dala biliyan 19.89 zuwa ƙarshen shekarar 2025.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version