Matatar man Dangote ta fitar da man jirgin sama da darajarsa ta kai kusan naira biliyan 757 zuwa Turai a watan Yuni. Adadin man da aka fitar ya kai tan 466,000, wanda ya yi daidai da kusan lita miliyan 582.5.
Rahotanni sun nuna cewa wannan ne mafi yawan man jirgin sama da Najeriya ta taɓa fitarwa zuwa Turai tun bayan da matatar Dangote ta fara samar da irin wannan mai a shekarar 2024. Haka kuma, Najeriya ta zarce Amurka wajen samar wa Turai wannan nau’in mai a watan Yunin.
Masana sun bayyana cewa wannan ci gaba na nuna yadda matatar Dangote ke ƙara faɗaɗa fitar da kayayyakin mai daga Najeriya tare da ƙarfafa matsayin ƙasar a kasuwannin makamashi na duniya. Najeriya ta fitar da tan 466,000, yayin da Amurka ta fitar da tan 399,000 a watan Yuni.
