Jam’iyyar ADC ta rusa shugabancinta na Jihar Kano tare da kafa kwamitin riƙon ƙwarya da zai jagoranci harkokin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zaɓen shugabanni. Mataimakiyar shugabar jam’iyyar ta ƙasa mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Hajiya Najaatu Muhammad, ce ta sanar da hakan a ranar Litinin yayin taron manema labarai a Kano.

Najaatu ta bayyana cewa an naɗa Alhaji Umar Bala a matsayin shugaban kwamitin riƙon ƙwaryar. Ta ce matakin ya yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar, kuma an ɗauke shi ne domin dawo da daidaito, tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin jam’iyyar da kuma cike giɓin shugabanci da ya taso a jihar.

Ta kuma yabawa mambobin ADC na Kano bisa gudummawar da suka bayar wajen bunƙasa jam’iyyar. Kakaki24 Online Newspaper ta ruwaito cewa shugabancin ƙasa na jam’iyyar ya tabbatar da cewa yana matuƙar daraja jajircewa da sadaukarwar mambobinta a jihar Kano.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version