Bilkisu Rabe Abubakar, yar tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar, ta ce iyalansu na cikin matsanancin tashin hankali bayan rasuwar mahaifinta a hannun ’yan bindiga. Ta bayyana cewa an yi jana’izar marigayin ne a ranar Asabar da misalin karfe 6:15 na yamma bayan an yi masa sallar jana’iza a Masallacin GRA da ke Katsina.
Ta kuma bayyana cewa har yanzu mahaifiyarsu, wadda aka sace tare da marigayin, na hannun masu garkuwa da mutane. Sai dai hukumomi sun tabbatar da cewa suna ci gaba da kokarin ganin an kubutar da ita cikin koshin lafiya.
An sace Manjo Janar Rabe Abubakar da matarsa ne a watan da ya gabata bayan harin da ’yan bindiga suka kai kan motarsu a Jihar Katsina. BechiHausa ta ruwaito cewa mahukuntan jihar sun ce marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka hada da ciwon suga da hawan jini yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane.
