Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarun Operation HADIN KAI sun samu nasarar dakile wani yunkurin kutsen ’yan ta’adda tare da lalata hanyoyin da ake amfani da su wajen samar musu da kayan aiki a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

A cewar rundunar, sojoji sun yi gaggawar mayar da martani bayan gano motsin wasu ’yan ta’adda da ke kokarin isa cibiyar horas da sojoji da ke Buni Yadi a ranar 9 ga watan Yuni. Sojojin sun bude musu wuta tare da fatattakar su, inda aka gano gawar ’yan ta’adda biyu da kuma babur daya a wurin.

Haka kuma, wani samame na sirri da aka gudanar a yankin Damboa ya kai ga kama wasu da ake zargi da samar wa kungiyoyin Boko Haram da ISWAP kayan aiki. BechiHausa ta ruwaito cewa rundunar sojin ta ce wadannan nasarori na nuna kudurinta na karya hanyoyin tallafa wa ’yan ta’adda da tabbatar da zaman lafiya a Arewa maso Gabas.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version