Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton Lakurawa ne sun kai wa sojojin Najeriya hari ta kwantan ɓauna a jihar Kebbi, inda suka kashe mutum 13 tare da jikkata da dama. Harin ya faru ne a daren Talata a garin Giro Masa da ke ƙaramar hukumar Shanga.
Rahotanni sun ce sojojin na kan hanyarsu ta kai ɗauki ne bayan samun kiran gaggawa daga al’ummar yankin lokacin da aka kai musu farmakin. An bayyana cewa daga cikin waɗanda suka mutu akwai sojoji 11 da jami’in ɗansanda guda, yayin da wasu fararen hula suka rasa rayukansu sakamakon raunukan da suka samu.
Kakakin ‘yan sandan jihar Kebbi ya ce ba zai yi tsokaci kan lamarin ba kasancewar aikin na sojoji ne. A nasa bangaren, gwamnan jihar, Nasiru Idris, ya kai ziyara wurin da harin ya faru tare da duba waɗanda suka jikkata a asibiti.
