Hatsari ya rutsa da wata tankar gas a yankin Chisco da ke hanyar zuwa Victoria Island a birnin Lagos, lamarin da ya janyo cunkoson ababen hawa a safiyar Litinin. Tankar ta kife a kan hanya, inda hakan ya tilasta hukumar kula da zirga-zirga ta jihar (LASTMA) da sauran jami’an ceto fara aikin cire motar daga titin domin tabbatar da tsaro da sake bude hanyar.
Daraktan yada labarai na LASTMA, Mista Adebayo Taofiq, ya bayyana cewa dole ne a rufe babbar hanyar na ɗan lokaci domin gudanar da aikin cikin kwarewa da tsaro. Ya kuma roki direbobi su nuna haƙuri da bin umarnin jami’an da ke gudanar da aikin ceto.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya haddasa gagarumin tsaiko, inda wasu fasinjoji suka sauka daga motoci suka fara tafiya a ƙafafu saboda cunkoson. Wata direba, Jane Kenneth, ta ce ta makale a hanya tun ƙarfe 8 na safe ba tare da motsi ba.
Hukumar LASTMA ta tabbatar da cewa ana ci gaba da aikin cire tankar domin dawo da zirga-zirga yadda aka saba cikin kankanin lokaci, tare da tabbatar da cewa tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne babban abin da gwamnati ta fi mayar da hankali a kai.
