Hukumar Hisbah ta Jihar Kano za ta baza jami’anta domin tabbatar da tsaro a wuraren da za a gudanar da bukukuwan Mauludi a fadin jihar.

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar, Dakta Mujahid Aminuddeen, ne ya bayyana hakan, inda ya ce Hisbah za ta kuma tura jami’anta domin gabatar da maƙalu da lakcoci a yayin bukukuwan.

Ya ce hukumar za ta sanya ido kan ɓata gari, tare da ɗaukar mataki kan duk wanda aka samu yana ƙoƙarin fakewa da bikin Mauludi domin aikata abubuwan da ba su dace ba.

Dakta Mujahid ya ƙara da cewa za a tsaurara irin wannan mataki a yayin bikin Takutaha, yayin da hukumar ta yi wa al’ummar Musulmi fatan gudanar da bukukuwan Mauludi lafiya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version