Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta ce tsarewa da gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ba shi da alaƙa da siyasa, illa bin doka. Kakakin hukumar, John Odey, ya bayyana cewa El-Rufai na hannunsu ne bisa umarnin kotu, yana mai jaddada cewa ICPC ba ta fifita ko nuna wariya ga kowane ɗan siyasa.

Wannan na zuwa ne bayan ƙungiyar magoya bayan El-Rufai ta sanar da ɗaukar wani kamfanin masu fafutukar kare dimokuraɗiyya da ke birnin Washington DC domin wayar da kan jami’an gwamnatin Amurka da sauran hukumomin duniya kan abin da ta kira tauye doka da kuma rashin bin ka’idojin shari’a a Najeriya.

Ƙungiyar ta ce tana kallon shari’ar El-Rufai a matsayin gwaji ga sahihancin cibiyoyin dimokuraɗiyya gabanin zaɓen 2027, tana mai zargin ana amfani da hanyoyin shari’a wajen takura wa ‘yan adawa. BechiHausa ta ruwaito cewa El-Rufai na fuskantar tuhume-tuhumen cin amanar ofis, almundahana da zamba a lokacin mulkinsa, tare da wata shari’a da DSS ke yi masa kan zargin saurarar bayanan jami’an tsaro.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version