An ji karar harbe-harbe da sanyin safiyar Alhamis a kusa da filin jirgin sama na Diori Hamani da ke birnin Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar. Mazauna yankin sun shaida cewa harbe-harben sun fara ne da misalin ƙarfe shida na safe kuma sun ci gaba na tsawon sa’o’i.

Rahotanni sun nuna cewa karar harbe-harben na fitowa ne daga ƙofar shiga filin jirgin saman, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin. Har yanzu hukumomi ba su fitar da cikakken bayani kan abin da ya haddasa lamarin ba.

A watan Janairu na wannan shekara, mayakan da ke da alaƙa da ƙungiyar Daular Musulunci ta Sahel sun kai hari filin jirgin saman, amma dakarun Nijar tare da abokan aikinsu na Rasha sun dakile harin. Nijar dai na ci gaba da fuskantar barazanar hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a yankin Sahel.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version