Manyan manhajojin da ke sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa sun tabbatar da cewa aƙalla jirage huɗu sun ratsa ta mashigar Hormuz bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka da Iran.
Rahotanni sun nuna cewa jirgi na farko da ya bi ta mashigar na ɗauke da tutar Faransa kuma yana jigilar gas, yayin da wasu jirage uku masu ɗauke da tutar Saudiyya suka biyo bayansa. Hakan ya biyo bayan amincewar Iran da sake buɗe mashigar a ƙarƙashin yarjejeniyar zaman lafiyar.
A yarjejeniyar, Iran ta amince da buɗe mashigar Hormuz yayin da Amurka za ta janye takunkumin da ta kakaba wa tasoshin ruwan Iran. Mashigar Hormuz na da muhimmanci ga tattalin arzikin duniya, domin ta nan ne ake safarar kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur da ake fitarwa a duniya, lamarin da masana ke cewa ya nuna haɗarin dogaro da hanya guda wajen jigilar makamashi.
