Kungiyar SERAP ta shigar da kara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), bisa zargin almundahana da rashin bayani kan kashe ₦55.9bn da aka ware domin kayan zaben 2019.

SERAP ta bukaci kotu ta tilasta wa INEC bayyana cikakkun bayanai kan kudaden, ciki har da sunayen ‘yan kwangila, daraktocinsu da masu hannun jari, tare da dawo da duk wani kudi da aka salwantar. Kungiyar ta ce rashin gaskiya da rikon amana a irin wannan lamari na barazana ga ‘yancin ‘yan kasa na samun sahihin zabe.

Rahoton ya nuna cewa an biya fiye da ₦5.3bn kan na’urorin karanta kati ba tare da amincewar BPP ko FEC ba, haka kuma an yi wasu manyan biya-biye ba tare da takardun shaida ba. SERAP ta ce wadannan zarge-zargen keta amana ne ga kundin tsarin mulki da ka’idojin yaki da cin hanci, yayin da har yanzu ba a sanya ranar sauraron karar ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version