Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da cewa ta ƙi amincewa da ƙungiyoyi shida daga cikin sabbin ƙungiyoyin da ke neman rajista a matsayin jam’iyyun siyasa a Najeriya. Wannan na zuwa ne bayan nazarin da hukumar ta gudanar a taronta na ranar 30 ga Oktoba 2025 domin duba ci gaban shirin rajistar jam’iyyu tun bayan sanarwar da ta fitar a watan Satumba.
A cewar Sanata Sam Olumekun, kwamishina mai kula da bayanai da wayar da kan masu zaɓe, ƙungiyoyi takwas ne kacal daga cikin 14 da aka tantance a farko suka kammala shigar da dukkan takardunsu da bayanan da ake buƙata ta hanyar dandalin yanar gizon hukumar kafin ƙarewar wa’adin ranar 18 ga Oktoba. Wadannan ƙungiyoyin sun haɗa da All Democratic Alliance, Citizens Democratic Alliance, Abundance Social Party, African Alliance Party, Democratic Leadership Alliance, Green Future Party, National Democratic Party, da Peoples Freedom Party.
INEC ta bayyana cewa mataki na gaba shi ne tantancewa da tabbatar da cewa takardun da kowace ƙungiya ta gabatar sun dace da kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999 (wanda aka gyara), dokar zaɓe ta 2022 da kuma ƙa’idojin hukumar. Wannan mataki, a cewar hukumar, zai tabbatar da cewa kawai ƙungiyoyin da suka cika sharuddan doka ne za su samu lasisin zama jam’iyya.
Hukumar ta kuma jaddada kudirinta na tabbatar da gaskiya, gaskatacciyar hanyar siyasa, da kuma bunƙasa dimokuraɗiyya a Najeriya. A halin yanzu, INEC ta karɓi wasikun neman rajista daga ƙungiyoyi fiye da 170 da ke son zama jam’iyyun siyasa a kasar nan.
