Gwamnatin Jihar Jigawa ta karrama iyaye, tsoffin shugabanni, sarakunan gargajiya, ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar da suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar cikin shekaru 35.

Gwamna Umar A. Namadi ya bayyana hakan ne a saƙon musamman da ya fitar domin bikin cika shekaru 35 da ƙirƙirar Jigawa. An kafa jihar ne a ranar 27 ga Agusta, 1991, daga tsohuwar Jihar Kano, inda aka mayar da Dutse babban birninta.

Namadi ya ce bikin ya zama wata dama ta tunawa da waɗanda suka yi ƙoƙari wajen samar da jihar da kuma duba irin ci gaban da aka samu. Ya kuma yaba wa tsoffin gwamnonin soja da na farar hula, ‘yan majalisa, alkalai, ma’aikatan gwamnati da sarakunan gargajiya saboda gudunmawarsu.

Gwamnan ya buƙaci al’ummar Jigawa su ci gaba da kare zaman lafiya, ƙarfafa adalci, kare dukiyar jama’a da kuma saka jari ga matasa. Ya ce hanya mafi kyau ta girmama waɗanda suka kafa jihar ita ce kiyaye manufofin zaman lafiya, adalci, gaskiya da shugabanci nagari.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version