Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Muhammad Usman Zuru, ya rasu. Rahotanni sun ce ya mutu ne a wani asibiti a ƙasar Masar, inda yake karɓar magani kan wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.
An ce marigayin ya daɗe yana fama da wannan rashin lafiya, kuma an kai shi ƙasashen waje domin jinya bayan da yanayinsa ya tsananta kafin fara azumin watan Ramadan da ya gabata. Marigayin shi ne wakilin mazabar Zuru a majalisar dokokin jihar.
Wani mai taimaka wa gwamnan Kebbi kan harkokin sadarwa da dabaru, Idris Abdullahi Zuru, ya bayyana rasuwar a matsayin abin firgici da raɗaɗi. Ya ce gwamnati na tattara cikakken bayani, kuma za ta sanar da jama’a shirye-shiryen jana’iza tare da iyalan mamacin.

