Wani jigo na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya gargadi shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) karkashin jagorancin David Mark da su daina yada zarge-zargen da ba su da tushe kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ya ce ya kamata jam’iyyar ta fadi gaskiya maimakon jingina matsalolinta ga shugaban ƙasa.
Oyintiloye ya bayyana cewa Tinubu ba kotu ba ne da zai bada umarnin dawo da tsoffin shugabannin ADC, yana mai cewa hukuncin ya samo asali ne daga kotu. Haka kuma ya ce shugaban ba shi da hannu a rikicin cikin gida na jam’iyyar, yana mai shawartar ADC da ta gyara matsalolinta maimakon zargin wasu.
Ya kuma jaddada cewa hukuncin Independent National Electoral Commission (INEC) na kin amincewa da kowanne bangare na ADC ya biyo bayan umarnin kotu ne. A ƙarshe, ya ce zargin kafa tsarin jam’iyya guda a ƙasar ba gaskiya ba ne, yana mai cewa akwai jam’iyyu 21 da za su fafata a zaɓen 2027.

