Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce Najeriya na iya ajiye biliyoyin naira duk shekara idan aka rungumi tsarin majalisa ta wucin gadi. Yayin wata hira da gidan talabijin na Channels ranar Alhamis, Ndume ya nuna cewa kudin gudanar da majalisa a tsarin zama na dindindin yana da tsada sosai, musamman a lokacin da kasa ke fama da matsalolin kudi da tsaro.

Ndume ya ce za a iya tura kudaden da ake kashewa wajen kula da ’yan majalisa zuwa bangaren tsaro da sauran muhimman bukatun kasa. Ya bayyana cewa kasar ba za ta iya jure barnar kashe kudade ba yayin da ake fama da ta’addanci a Arewa maso Gabas, garkuwa da mutane, da karuwar laifuka a wasu yankuna.

Sanatan ya kuma soki ci gaba da kasancewar ’yan sanda a rakiyar ’yan siyasa da masu tasiri duk da umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye jami’an tsaro daga irin wannan aiki. Aminiya ta rawaito cewa Shugaban kasa ya umarci Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, da ya tura jami’an zuwa fagen yaki da ta’addanci da samar da tsaro.

Ndume ya jaddada cewa tsarin tsaron kasa ya yi kunci kuma yana bukatar hadin kai, inda ya ce dubban jami’an suna makale wajen rakiyar ’yan siyasa da masu tasiri wadanda za su iya rayuwa ba tare da irin wannan rakiyar ba. Ya kara da cewa tura ’yan sanda zuwa aikin al’umma zai kara inganta tsaron kasa fiye da mai da su rakiyar mutum daya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version