Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta karɓi jimillar ƙorafe-ƙorafe 12,446 daga al’ummar jihar a ƙananan hukumomi 44, daga watan Janairu zuwa Disambar 2025. Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton ayyukan hukumar na shekarar da ta gabata.

Rahoton, wanda Mataimakin Kwamandan Hisbah, Dakta Mujahiddeen Aminuddeen ya fitar, ya nuna cewa hukumar ta warware rigingimu 1,908 tare da aiwatar da ayyukan sintiri da tilasta bin doka guda tara a sassa daban-daban na jihar.

Haka kuma, Hisbah ta kama mutane 132 da ake zargi, tare da kula da manyan shari’o’i 4,246 a cikin shekarar. Rahoton ya ƙara da cewa sama da mutane 93,000 sun amfana da ayyukan hukumar, yayin da kuɗaɗen basussuka, tarar laifuka da diyya suka haura Naira miliyan 145.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version