Mutum huɗu ’yan gida ɗaya sun mutu, yayin da wasu 12 suka jikkata bayan ruftawar wani bene mai hawa biyu a unguwar Ɗandinshe Kwanar Yashi, da ke Ƙaramar Hukumar Dala a Jihar Kano.

Ginin, mallakin wani mutum mai suna Yusuf Officer, shi ne yake zaune a cikinsa tare da matansa uku da ’ya’yansa 12. Wani mazaunin yankin ya ce ana kan aikin hawa na biyu kafin ginin ya rufta a ranar Asabar.

Ya ce mazauna yankin da jami’an ceto sun kwashe kusan sa’o’i tara suna aikin ceto mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin. Hukumar Kashe Gobara ta Kano ta ce an samu nasarar ceto mutum 13 da ransu, ciki har da yara.

Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce an fara samun kiran neman agaji da misalin ƙarfe 4:32 na asubahin Asabar, inda aka tura jami’an ceto zuwa wurin. Ya ce ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin ruftawar, tare da yin kira ga mazauna yankin da su ƙara taka-tsantsan musamman a lokacin damina.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version