Sojojin rundunar Operation FANSAN YAMMA sun ceto fasinjoji 33 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Magazu, da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar, inda ’yan bindigar suka sace fasinjojin a yankin Magazu, lamarin da ya jawo ɗaukar matakin gaggawa daga jami’an tsaro.

A cewar rahoton Daily Trust, jami’an tsaron sojin sun haɗa gwiwa da jami’an rundunar ’yan sandan Najeriya da ke Tsafe domin kai ɗauki zuwa yankin da lamarin ya faru.

Haɗin gwiwar jami’an tsaron ya yi nasarar ceto fasinjojin 33 da aka yi garkuwa da su, bayan kai ɗaukin gaggawa zuwa yankin Magazu na Ƙaramar Hukumar Tsafe.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version