Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ceto wani mutum mai shekaru 40 tare da shanunsa, bayan sun makale a wata tsohuwar rijiya a ƙauyen Sabon Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Makoda.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 3:22 na yammacin Laraba.

Ya bayyana cewa Ibrahim Jibrin ne ya kai rahoton cewa wata saniya mai shekaru biyar ta faɗa cikin rijiyar. Mai shanun, Badamasi Ibrahim, ya yi ƙoƙarin shiga rijiyar domin ceto dabbar, amma shi ma ya makale kuma ya kasa fitowa.

Abdullahi ya ce jami’an hukumar sun garzaya wurin kuma suka samu nasarar ceto mutumin da saniyar da rai. Daraktan hukumar, Alhaji Sani Anas, ya gargadi jama’a da kada su riƙa shiga rijiyoyi domin ceto mutane ko dabbobi, yana mai ba da shawarar kiran jami’an ceto cikin gaggawa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version