Hukumar Zabe ta jihar Kano, Kano State Independent Electoral Commission (KANSIEC), ta mika takardar shaidar cin zabe ga Ali Musa Hardwoker, inda ta tabbatar da shi a matsayin halattaccen shugaban karamar hukumar Kumbotso.

Mai girma Shugaban Majalisar Dokokin jihar Kano, Ismail Jibrin Falgore, ne ya mika takardar shaidar ga Ali Musa Hardwoker, wanda hakan ke tabbatar da halartar sa a matsayin shugaban karamar hukumar. Wannan mataki na zuwa ne bayan hukuncin kotu da ta soke nasarar Abdullahi Basaf a zaben Kumbotso.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version